A wani mataki na tauna tsakuwa don baiwa aya tsoro, majalisar dokokin kasar Saliyo ta amince da dokar hukuncin kisa kan duk wani wanda aka kama da aikata manyan laifuka a kasar.
Kazalika z a iya maye gurbin hukuncin kisan da daurin rai da rai a gidan yari, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Idan za a iya tunawa a watan Mayu ne mataimakin ministan shari’a na kasar ya sanar da kudirin wanzar da babban hukunci ga masu aikata manyan laifuka.
Sai dai Kungiyoyin duniya sun ce akwai hukunce-hukuncen kisa da aka yanke har guda 39 a kasar a shekarar da ta gabata, amma babu guda da aka wanzar tun bayan shekarar 1998.
An sh ganin kasar na garambawul ga wannan doka ta hukuncin kisa a kasar, to amma wajen aiwatar ne ke zama tamkar an aiki bawa garinsu.
Yanzu haka dokar na jiran sanya hannun Shugaban Kasar ne Julius Maada Bio wanda zai sa kasar ta zamo ta 23 da ta wanzar da dokar hukuncin kisa a tsakanin kasashen Afirka.