Shahararren attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote, ya kai ziyara ta musamman ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasan Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Ziyarar Dangote na zuwa ne kafin zuwan ranar 29 ga watan Mayun 2023, wacce za a rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban kasan Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Jami’ar Bayero a Kano (BUK) ta yi rashin rajistara
Jaridar Legit.ng ta tattaro cewa shafin zaɓaɓɓen shugaban ƙasan na Twitter, shine ya tabbatar da ziyarar da Dangoten ya kai a ranar Laraba, 26 ga watan Afirilu.
Tinubu ya karɓi baƙuncin Aliko Dangote, attajirin da ya fi kowa arziƙi a nahiyr Afirika, tare da kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Femi Gbajabiamila, da tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasa (EFCC), Malam Nuhu Ribadu.
Sauran waɗanda suke a wurin lokacin ziyarar sun haɗa da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, Hon. James Faleke da Ibrahim Masari.
Duk da dai cewa abokan takarar Tinubu na ƙalubalantar nasarar sa a gaban kotu, ana sa ran za a rantsar da shi domin karɓe ragamar mulki a hannun shugab Buhari, a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Najeriya Ta Kashe Dala Miliyan 1.2 Domin Yan Kwashe Yan Kasar Daga Sudan
Gwamnatin Tarayya, ta ce ta kashe dala miliyan 1.2 don tura motocin bas guda 40 don kwashe akalla ‘yan Najeriya 2,400 da suka makale daga Sudan.
Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, ne ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya na wannan mako wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jagoranta a zauren majalisar da ke Aso Rock Villa, Abuja.
The Chouse Of God Is The Best