Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta ƙaddamar da wata manhajar da jama’a za su damar fallasa laifukan cin hanci da rashawa a kasar.
Kamar yadda Shugaban Hukumar Abdulrashid Bawa ya bayyana yayin kaddamar da manhajar, ya ce za ta taimaka matuka wajen shirin yaki da cin hanci da rashawa da ake fama da shi a faɗin Najeriya.
Bawa wanda ya ce manhajar ya Eagle Eye zata taimaka sosai wajen tabbatar da sakaye mutane da ke da aniyar fallasa duk wani cin hanci da ake yi.
Ya ce “Gaskiya muna alfahari da wannan manhaja kasancewarta dan kasa ne ya kirkiro ta”
“Manhajar Eagle wata baiwa ce ga hukumar EFCC da kuma kasa baki ɗaya, kuma za mu yi aiki da ita yadda ta dace” Cewar Bawa.
Ya ce ta hanyar amfani da Eagle Eye, yan Najeriya da ma wadanda ba yan Najeriya ba na da damar daukar hoton duk wata badakalar vin hanci dake wakana a ko ina a fadin kasar.
Sai dai Abdulrashid Bawa ya ce inda gizon kw saka shine amfani da asusun bogi da yan kasa ke yawan amfani da shi, don haka ya hori yan kasar da su guji wannan mummunar dabi’a.