Hukumar Hana Fasa Kauri ta Kasa Kwastam a Jihar Ogun ta ce ta chafke tireloli guda talatin da takwas makare da buhunan shinkafa kimanin dubu goma sha tara yar kasar waje.
Wannan Kame da Kwastom ta yi a watanni uku na farkon Wannan Shekara, an ƙiyasta kudin shi zai kai sama da naira miliyan dari uku.
Kwanturola mai kula da shiyar Ogun Peter Kolo wanda ya bayyana haka wa manema labarai a birnin Abekuta a yau talata inda ya ce shinkafar an shigo da su ne ta ɓarauniyar hanya inda suka yi amfani da Motar Kamfanin Coca-cola.
Kwanturolan ya bayyana matukar Kaduwar shi jisa yadda ake amfani da ababen hawa na manyan Kamfanoni wajen Safarar kayan Abincin daga ƙasashen ketare, amma ya ce duk wanda aka chafke da yin hakan to lallai zai yaba wa aya zakin ta.
Ya kara da cewa, hukumar ta tara kudin shiga da ya kai naira miliyan takwas a watan Maris kadai, tare da chafke Kayyaki daban-daban da aka yi safarar su da suka hada da man fetur da muggan kwayoyi da motoci da kuma babura wajen safarar su.
Da ya hada jimillar kudin shiga da hukumar ta tara a watanni ukun farkon wannan shekara, ya ce ya kai naira miliyan sha biyu da dori.