Shahararren dan damben zamani na Boxing din nan dan Najeriya mai matsakaicin nauyi Israel Adesanya ya kalubalanci dan damben zamani na duniya Robert Whittaker da su fito su sake kwafzawa.
Toh sai dai wannan karon ya ce idan za su kara kamata ya yi su samu sabon wuri ne da ba su taɓa kece raini a wurin ba kamar birnin Auckland na New Zealand.
Shi dai Adesanya wanda ya kware a salon kwanta-kwanta ya masge dan kasar Italiyar nan Marvin Vettori a ranar Lahadi a wani gumurzu da suka a birnin Arizona, lamarin da ya sa yake ci gaba da kare kambunsa na uku.
Kazalika shine dan wasa na farko da ya kasa yan wasan Boxing dake matakin biyar din farko a duniya, kuma yana so ya ci gaba da hakan a kowanne mataki da ya tsinci kansa.
Idan ba a manta ba, Adesanya ya wargaza Whittaker a shekarar 2019 al’amarin da ya sa ya lashe gasar damben Boxing na masu matsakaitan nauyi.
Wata kila wannan ne ya kara mishi kwarin gwiwar neman sabon raba raini tsakaninsu, domin an ce mai laya ya Kiyayi Mai Zamani.