Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana kansa a matsayin mutum mai sa’a duba da irin muƙaman da ya riƙe kafin ya zama shugaban ƙasa.
Shugaban ƙasar ya kuma roƙi gafarar mutanen da ya ɓatawa rai a dalilin wasu daga cikin tsare-tsaren sa da su yi haƙuri shi ma ɗan Adam ne. Jaridar The Punch ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Rashin Tausayi: Mijina Yana Lakadamun Dukan Tsiya, Yana Barazanar Hallaka Iyayena— Matar Aure
Shugaban Buhari yana da kusan ragowar kwana 36 a kan kujerar mulki kafin cikar wa’adin mulkin sa.
Da yake magana lokacin da ya karɓi baƙuncin baƙin da suka je masa yawon Sallah na ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa a fadar da da ke Villa Abuja, shugaba Buhari ya bayyana kansa a matsayin mutum mai sa’a, inda ya taɓa gwamnan jihar Borno a mulkin soja a shekarar 1976, ministan albarkatun man fetur a cikin wannan shekarar, da kuma shugaban ƙasa a mulkin soja.
A kalamansa:
“Ina kallon kai na a matsayin mai sa’a sosai. An yi min gwamna, ministan man fetur, shugaban ƙasa a mulkin soja, daga nan bayan jarabawa sau uku, Allah ubangiji ta hanyar fasaha da PVC ya sanya na zama shugaban ƙasa. Ina ganin Allah ya bani babbar damar zama shugaban ƙasa. Ina godiya ga Allah bisa bani wannan damar.”
Rundunar Yan Sanda Ta Kori Wasu Jami’anta Mutum 18
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kori ‘yan sanda akalla 18 bisa samun su laifuka daban-daban da suka hada da cin zarafi da rashin da’a da kuma karbar kudi.
Wannan bisa ga nazarin rahotannin kafofin watsa labaru da ke nuna adadin ‘yan sandan da aka kora a watan Oktoba da Disambar shekarar 2022, da Afrilu, 2023.