Tawagar kasar Italiya ta lashe kofin Nahiyar Turai na EURO 2020, bayan ta farfado da ga bisa, wanda ta yi nasara a kan Tawagar Burtaniya a bugun daga kai sai Mai tsaran gida, wanda aka fa-fa-ta jiya Lahadi, a Filin wasa na Wembley .
Nasaran da Italiya ta yi, shine karo na farko tun bayan lashe kofin da ta yi a shekarar alif 1968, Kuma shine kofin da ta lashe na farko tun bayan nasaran lashe kofin Duniya (World Cup) a shekarar 2006.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jihar Kaduna ta yi rashin masoyin Talakawa ~ Sanata Uba Sani
Dan wasa Luke Shaw ne ya fara jefa wa Tawagar England kwallon farko, mintina kadan da fara wasan, inda bayan dawo wa hutun rabin lokaci ne, Leonardo Bonucci ya farke wa Italiya wannan Kwallo.
Da fari dai England ce ta fara shigewa gaba, a bugun daga Kai sai Mai tsaran raga, Amma daga bisani ta gaza gefa kwallo ko daya, a cikin bugu uku da ta buga, inda Mai tsaran ragar Italiya Gianluigi Donnarumma, ya ture kwallaye biyu, daya kuma ta bigi Tirke, hakan yasa aka tashi wasan 3 da 2
Ga gerin sunayen kasashen da su ka taba lashe gasar na Zakarun Nahiyar Turai, tun bayan fara gasar.
A shekarar 2020: Italiya (Italy)
A Shekarar 2016: Fotugal (Portugal)
2012: Sifaniya (Spain)
2008: Sifaniya (Spain)
2004: Girka (Greece)
2000: Faransa (France)
1996: Jamus (Germany)
1992: Dalmak (Denmark)
1988: Nedalan (Netherlands)
1984: Faransa (France)
1980: Yammacin Jamus (West Germany)
1976: Cekolobakiya (Czechoslovakia)
1972: Yammacin Jamus (West Germany)
1968: Italiya (Italy)
1964: Safaniya (Spain)
1960: Tarayyar Sobiyat (Soviet Union)