An shiga halin dimuwa da firgici a Kaduna bayan da jami’an tsaro suka yi ta harbin ƴaƴan Ƙungiyar yan uwa musulmi dake zanga-zanga, a wani yunkuri na tarwatsa taron.
Masu zanga-zangar sun fito ne suna ci gaba da nuna mubaya’ar su da a saki jagoran su Sheikh Ibrahim Elzakzaky.
Jim kaɗan bayan samun rahotannin masu zanga-zangar ne dai jami’an tsaron suka yi fita ta farin ɗango inda suka nufi Babbar kasuwar Central Market dake birnin Kaduna inda nan ne masu zanga-zangar suka dunguma.
Ko da yake rahotanni sun tabbatar da cewa bayan yayan kungiyar yan uwa musulmin sun watse daga zanga-zangar jim kadan bayan hango Jam’ian yan sandar da motocinsu.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar ta Kaduna ASP Muhammad Jalige ya kasa cewa uffan game da lamarin inda ya ce sai ya tuntubi rundunar dake kula da yankin.