Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria Kano (MAAUN) ta yaba wa shahararriyar Mawakiyar Hausa magayiya Magajiya Dambatta Makoda, bisa gagarumar gudunmawar da ta bayar wajen shiga Harkoki makaranta da kuma gudunmawar da ta bada wanda ba zai misaltu ba a fannin ilimi. Jami’ar ta sanyawa daukacin sashin shari’a sunan Mawakiyar.
A cewar wani mai fafutukar ci gaba a Kano, Malam Abdullahi Sufi, cikin sauki za a iya gane magayiya Magajiya Dambatta Makoda a matsayin mutumiyar da ta tashi da kanta don ta zaburar da mutane kan abin da ta yi imanin zai yi musu amfani. Ya bayyana cewa irin wannan karimcin da jami’ar ta yi mata ya yi daidai da masu hannu da shuni, fitattun mutane, abokai, ‘yan uwa ko sau da yawa ana ba da su don kashin kai.
‘Wannan wani ci gaba ne na gine-ginen da jami’ar ta sanyawa sunanta, Makarantar koyon aikin lauya ta Magajiya Dambatta Makoda dake jami’ar MAAUN Kano, domin irin gudun Mawar da Magajiya ke bayarwa a fannin ilimi wanda ya kai ga samar da karin wadanda suka kammala karatu a dukkan fannonin ilimi. kokarin mutane daga yankin Arewa,” in ji Sufi
Comments 1