Matashiyar Jam’iyyar nan ta matasa wato Young Progressive Part a Jiher Ribas, ta biya wa kurame da makafi gami da wasu mutane masu fama da nakasa kimanin su dari kudin rubuta jarabawar shiga manyan makarantu wato JAMB na wannan shekara.
Shugaban Jam’iyyar, Kwamared Anthony Attah shi ya sanar da hakan a yayin ganawarsa da ƴaƴan Ƙungiyar Makafi da kurame ta Jihar Ribas, wanda ya wakana a babban Makarantar Masu Bukata ta Musamman dake birnin Kalaba.
A yanzu haka ya ce jam’iyyar za ta fara wani rangadin baiwa mambobin ta katin zama dan jami’ya wa mutane dubu biyar.
A bangaren sa Shugaban Ƙungiyar Kurame da Makafin, ya jinjina wa Jam’iyyar bisa wannan nauyi inda ya yi mata addu’ar fatan Alkhairi