Gwamnatin tarayya ta ce kamfanin tuwita ya kawo mishi tayin sulhu tsakani, biyo bayan haramcin da gwamnatin tarayyar ta yi kan ayyukan kamfanin a Najeriya.
Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Muhammad shi ya bayyana haka a yau Laraba yayin zantawa da yan jaridan gidan Gwamnati a birnin tarayya Abuja.
Ya ce a yanzu haka kamfanin na tuwita ya kadu matuka musamman irin yadda yake hasarar kudade masu dumbin yawa sakamakon wannan haramci da gwamnatin tarayya ta yi.
To sai dai Lai Muhammad gwamnatin tarayya ba za ta karɓi wannan tayi ba har sai kamfanin ya yi rajista a Najeriya, duba da irin amfana da yake yi da kasar nan, kana ba za rika wuce gona da iri ba.
Da yake magana kan harajin da kamfanonin sadarwar zamani ke yi, Lai Muhammad ya ce galibinsu na aiki ne ba tare da bada ko kwandala ba.
Yanzu haka dai gwamnatin tarayya ta gindaya wasu sharuda ga manyan Kamfanonin sadarwa a kasarnan da dole sai sun bi gabannin ci gaba da aiwatar da ayyukansu.