Ka binciki Mutuwar Mahaifina — Kiran Ɗan Gidan MKO Abiola ga Buhari
Abdul Abiola, ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayi Chief MKO Abiola ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daya binciki abinda ya haddasa mutuwar mahaifin sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Wani Sarki a Ilori ya buƙaci Gwamna Abdulrazaq ya nemi wa’adi na biyu
Abiola ya yi kiran ne ga Shugaban Ƙasa ta hanyar wani rubutu daya fitar a shafin sa @AbdulMKO a ranar Talata.
Ya buƙaci Buhari daya Duba kundin ajiye bayanai na Najeriya tare da bayyana gaskiyar abinda ya faru, yana mai cewa yanzu lokaci ne da ƴan Najeriya ya kamata su san abinda ya haifar da mutuwar.
A cewar sa, gaskiyar zata taimaka wajen yin Adalci.
Ya rubuta “lokaci ne daya kamata mutanen Najeriya su san gaskiyar abinda ya faru a zaɓen 12 ga watan yunin Shekarar Alif 1993.
“Tare da gano abinda ya haddasa mutuwar MKO Abiola da Kudirat Abiola da wasu.
“Ina kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daya Duba kundin ajiye bayanai na kasar tare da sanar da abinda ya faru don Adalci.”
Comments 1