Mutane da dama sun sha mamaki bayan ganin wani tarihi da iyalan wani mamaci suka rubuta wanda ya rasu yana da shekaru 66 a duniya, Legit.ng ta ruwaito.
Samuel Strong ya wallafa tarihin ta shafi a na Facebook a wani rukuni mai suna Rant HQ Extention kuma ya yi wani tsokaci inda yace ya mata su bar shi ya kwanta ya huta.
KU KARANTA: An sha mamaki yayin da ɗaliban sakandare suka ba malaminsu kyautar bulala ranar aurensa
Yaran mutumin sun ce duk da dai babu wanda ba ya da wata matsala a rayuwarsa, amma bai bar musu wani abin a yaba ba.
Sun kwatanta shi a matsayin inuwar giginya, inda mutane waje ne kadai ke jindadinsa.
Sun ce sun yi danasanin kasancewa ‘ya’yansa. Amma yanzu kuma ga shi kwance suna kallonsa a mace.
Ya sharbi kuka: Yadda matashi ya kai wa budurwarsa ziyara bazata, ya sha mamakin abin da ya gani
Wani matashi ya sha kuma bayan kai wa budurwarsa ziyarar ba zata inda ya ga abinda yayi matukar daga masa hankali har ya kasa hakuri yayi wallafa a soshiyal midiya, Legit.ng ta ruwaito.
Wannan wallafar ta sa mutane da dama sun dinga kwanta masa da hankali inda su ka ba shi shawarar ya bar ta ya ci gaba da rayuwarsa.
Ya wallafa hirar ne a Twitter inda yace bayan isar sa gidan ba tare da sanar da ita ba, ya dade yana kwankwasa kofa amma be ji amsa ba.