Kada ku Zaɓi Atiku, Domin hakan zai wargaza haɗin kan Najeriya — Jigon APC ga Ƴan Najeriya
Wani jigon jam’iyyar APC a jihar Legas, Joe Igbokwe, ya gargadi ‘yan Najeriya game da takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP na Atiku Abubakar.
Igbokwe ya yi gargadin cewa takarar Atiku za ta yi illa ga hadin kan Najeriya.
Ya jaddada cewa takarar Atiku kamar sanya wuka ne a kan abubuwan da suka hada Najeriya tun 1960.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za’a dakatar da Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi kan karɓar Bashi a Jihar Neja
Mai ba Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas shawara na musamman kan harkokin magudanun ruwa da albarkatun ruwa ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook ranar Laraba.
Ya ci gaba da cewa dole ne Kudu ta samar da shugaban kasar.
“Wadanda har yanzu suke ingiza Atiku Abubakar ya tsaya takara a 2023, kullum suna sanya wuka mai kaifi kan abubuwan da suka hada mu a matsayin kasa tsawon shekaru 62.
Igbokwe ya rubuta cewa “Dole mulki ya koma yankin Kudu a 2023.”
Zaben shugaban kasa na 2023 shine karo na biyar da Atiku yayi yunkurin mulkin Najeriya.
Atiku dai ya taba tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyu da dama a baya.
Dan shekaru 75 ya samu tikitin PDP a 2019 amma ya sha kaye a hannun shugaba Buhari na APC.
Sai dai Atiku zai fuskanci manyan ‘yan takara kamar Bola Tinubu na APC, Peter Obi na Labour Party, LP, Rabiu Kwankwaso na New Nigeria Peoples Party, NNPP, da dai sauransu.
A wani labarin kuma: Zaɓen 2023: INEC zata fara ɗaukar Ma’aikatan Wucin Gadi
A ci gaba da shirye-shiryen tunkarar Babban zaɓe na 2023, Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasa INEC ta fara shirin ɗaukar ma’aikata na wucin gadi na babban zaben 2023.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba a shafinta na Facebook, ta bukaci masu sha’awa da masu cancanta su ziyarci adireshin yanar gizo da ta samar.