Kada ku zamo Makaman da ƴan siyasa zasu riƙa amfani daku don ruguza Najeriya — Ɗan Majalisa ga Matasa
An tuhumi matasa a jihar Osun da kada su bari ƴan siyasa su yi amfani da su a matsayin ƴan daba ko kuma wakilan tada zaune tsaye.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan sanda sun kama Ɗan damfara da yake sajewa a Matsayin Matafiyi a Legas
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Osun ne ya bayar da wannan umarni a ranar Litinin a zauren Majalisar.
Owoeye ya kuma jajanta wa Kofoworola Babajide, Shugaban Marasa Rinjaye na majalisar kan harin da aka yi wa gidan mahaifinsa a karshen mako.
Yayin da yake yin Allah wadai da siyasar bacin rai, Shugaban Majalisar ya umarci masu riko da iyaye da su tabbatar da cewa ɗiyansu ba su da wata makarkashiya wajen haddasa hargitsi da lalata zaman lafiyar da Jihar ta samu a kan siyasa.
“Ina so in tuhumi matasanmu da kada su bari a yi amfani da su a matsayin masu kawo tarnaki. Kada ku bari a yi amfani da ku a matsayin ƴan fashi da makami, ku tabbatar da zaman lafiyar da aka san Jihar da shi.
“Ya kamata a kiyaye zaman lafiyar da aka samu a gabanin Gwamnatin Gwamna Oyetola da kuma lokacin Gwamnatinsa domin kada jihar ta wargaje.
“Ina so in umarci iyaye da su ci gaba da jagoranci tare da sanya ido a yankunansu a faɗin Jihar, don kada matasa su shiga cikin ƴan daba ko duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiyar Jihar a kan al’amarin siyasar tuggu,” inji shi.