Karkatar da kuɗaɗen Kananan Hukumomi ba zai yiwu ba sai da sanin EFCC da ICPC – Shehu Sani
Tsohon dan majalisar dokokin Najeriya, Sanata Shehu Sani, ya yi tir da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, kan karkatar da kudaden kananan hukumomi ga gwamnatocin jihohi.
Sanata Sani ya bayyana damuwarsa ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter da aka tabbatar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kirkirar Ƴan sandan Jihohi zai magance matsalar rashin tsaro – Uba Sani
Ku tuna cewa a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta zargi gwamnonin jihohi da karkatar da kudaden kananan hukumomi.
Shugaban kasar ya yi wani taron a ranar Alhamis ya yi zargin cewa wasu gwamnonin jihohi suna karkatar da kason kudi zuwa kananan hukumomin da aka aika daga asusun tarayya.
Sai dai Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya yi fatali da wannan ikirari da Gwamnatin Tarayya ta yi, inda ya ce kamata ya yi ta fito fili ta hanyar bayyana sunayen wadanda suka aikata laifin, maimakon yin tuhume-tuhume.
A halin da ake ciki kuma, Sani, wani fitaccen mai sukar lamirin al’umma ya yi wani ra’ayi na daban, yana mai cewa ba zai yiwu a karkatar da kudaden kananan hukumomi ba tare da sanin EFCC da ICPC ba.
Ya rubuta: “Ba zai yiwu a karkatar da kudaden kananan hukumomi zuwa ga gwamnatocin jihohi ba tare da sanin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ba.
“Babu wani makudan kudade da za su iya tafiya a cikin tsarin banki ba tare da gaggafa ko idanu ba. Idan suna son dakatarwa za su iya.
A wani labarin kuma: Kirkirar Ƴan sandan Jihohi zai magance matsalar rashin tsaro – Uba Sani
Sanata Uba Sani, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kaduna a zaben badi, ya bayyana cewa samar da ‘yan sandan jihohin kasar nan ba karamin abu ba ne zai taimaka wajen magance kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta.
Dan takarar gwamnan wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen jihar Kaduna, ya bayyana cewa kasancewar haramtattun makamai a fadin kasar nan abu ne mai matukar tayar da hankali kuma rashin tsaro ya karu a sassan kasar.