Tawagar kasar Jamus ta yan kasa da shekara 21 ta lashe gasar Euro na shekara ta 2021 bayan doke kasar Portugal ci 2:1.
Kwallon da dan wasan Manchester City Lukas Nmecha ya zura shi ya baiwa Jamus din damar jijjiga wannan kofi karo na uku.
Yanzu haka wannan rashin nasara ya sa Portugal ta yi rashin nasara wasan karshe har sau uku kenan da ta buga a gasar.
Yanzu dai abinda zura ido a gani shine yadda za ta kaya a gasar Euro 2020 ta manya wanda za ta gudana daga ranar Juma’ar makon gobe.