A wani rahoto da aka gabatar, Kaso tamanin cikin kananan asibitoci casa’in dake jahohi sha biyar dake kasar nan basu cika ka’idar da hukumar dake kula da kananan asibitoci ta (NPHCDA) sanya ba, kamar yadda kungiyar CODE ta ruwaito. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
A wani babban taro da aka gudanar a garin Jos, Khadijah Muhammad Abdulhameed, tace, anyi binciken haka ne tun wata uku da suka gabata a Jahar.
Khadijah Muhammad tace Conrad Hiltop Foundation da Skol Foundation ne suka dauki nauyin binciken.
KARANTA:- Kulawa da dokar hanya bata hukumar FRSC kadai bane yana kan kowane mutum
Tace an gudanar da binciken ne a yankuna shida dake kasar nan.
“Biyu daga kowane goma na jahohin basa da isashiyar wutar lantarki, suna dai amfani da tocila ne.
“Kaso talatin basa da ruwan sha mai kyau, wasu suna dogaro da rijiya ne ko ruwan sama a matsayin hanyar samar da ruwansu.”
“Ta fannin ajiye Magunguna, hamsin da shida ne cikin casa’in suke da firizan adana Magungunan.”
A kuma wani rahoto da Sakataren hukumar dake kula da kananan asibitoci Livinus Muapkwap, ya gabatar a wajan taron, yace gwamnati na iya bakin kokarin su wajan samar da kayayyaki da za su tallafawa Asibitocin.
Daga karshe dai wasu bangaren Mutanen sun shawarci hukumar dake kula da kananan asibitoci da su samar da Jami’ai da za su sanya idon akan ayyukan Asibitocin don ganin sun kai matakin da ake so.
A wani labarin
Shugaban kwamitin amintattu na PDP ya koma APC
Sanata Joy Emordi, daya daga cikin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar adawa ta PDP ya fice daga Jam’iyyar inda ya koma APC.
Sanata Joy Emordi, ya sanar da komawarsa APC ne a yau Laraba a Abuja.
Shugaban Jam’iyyar APC na rikon kwarya gwamna Mai Mala Buni, ya karbeshi a Abuja.
Ciki dai harda tsohon shugaban majalisan dattijai Ken Nnamani; da gwamna Atiku Bagudu na Jahar Kebbi; da gwamna Abubakar Badaru na Jahar Jigawa.
Kamar yadda wani jawabi da Mamman Mohammed, yace Emordi ya aminta da cewa hadin kan Nigeria da zaman lafiyar kasar ya rataya ne a wuyan Jam’iyyar APC.
Ya siffata jam’iyyar ta APC a matsayin jam’iyya mai tsari, wadda take da nufin kawo cigaba a kasa.
Gwamna Mai Mala Buni, yace shigowar Emordi zai kara hada kan al’ummar kasar nan, musammanma na yankin kudu.
Joy Emordi ya sanar da ficewa Jam’iyyar ta PDP ne washe gari bayan mutane bakwai sun bar jam’iyyar.
Sai dai shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Uche Secondus, na fuskantar matsi daga mutanensa kan yadda mutane keta ficewa daga Jam’iyyar.