Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari ya janyo hankalin shuwagabanni kan wadata matasa da ayyukan yi, hakan na daga cikin hanyoyi da zai rage matsalar tsaro dake addabar kasar nan.Jaridar Guardian ta wallafa a shafinta
Gwamna Aminu Bello Masari yayi wannan kira ne ta hannun Alhaji Ibrahim Musa Kalla, babban Sakataren mataimakin gwamnan Jahar Katsina.,
Gwamnan yace, baiwa matasa hanyoyi daban-daban zai hanasu fadawa cikin muggan ayyuka.
KARANTA:- NDLEA sun cafke shugaban kungiyar NURTW tare da mutane 3 kan laifin safarar miyagun kwayoyi
Kamar yadda yace, ” Wajibin mune mu ciyar da yankinmu gaba, muna da bukatar masu hannu da shuni sun fara tallafawa matasa dake yankunan mu.”
Wajibin Kungiyoyi masu zaman kansu, da daidaikun mutane da wasu Hukumomi su cigaba da sanya hannu a cikin wannan lamarin.
Gwamna Masari yace ingantacce ilimi gami da taimakawa matasa shine kawai zai hana matasa fadawa cikin muggan ayyuka.
“Idan muka ilimantar da matasa zamu rage yawan masu garkuwa da mutane, mu fara daukan dawainiyar karatun wasu dake yankinmu domin tallafawa garuruwan mu.
A wani labarin, Ruwaya cinye wani Matashi a Kano
Hukumar dake kashe gobara ta Jahar Kano, ta tabbatar da mutuwar wani Matashi mai suna Yusuf Aliyu, mai kimanin shekaru ashirin, inda ruwa ya tafi dashi a Danbare, Layin Bakar Lamba a Kano.
Hukumar ta sanar da hakane, ta wani bayani da ya fito ta hannun mai kula da huldan jama’a, Alhaji Saminu Abdullahi a Kano, a ranar Asabar.
Yace “mun sami wani kira na gaggawa daga Danlami Danladi misalin karfe hudu saura kwata na yammacin ranar Juma’a.”
“Yake shaida mana cewar akwai wani Matashi wanda ruwa ya tafi dashi, Nan take bayan mun kammala wayar dashi muka tura jami’an mu da misalin karfe hudu da minti biyar.” kamar yadda ya bayyana.
Alhaji Saminu Abdullahi yace koda muka fiddo da Yusuf Aliyu ya rigaya ya mutu.
Yace nan take muka mika gawar ga mahaifinshi Aliyu Sufiyanu.
Alhaji Saminu Abdullahi yace ana cigaba da bincike don gano musabbabin aukuwar lamarin.
Comments 1