Dan wasan tsakiya na Manchester City Kevin de Bruyne zai hade da tawagar yan wasan Belgium a ranar Litinin bayan da aka mishi tiyata.
de Bruyne wanda ya gamu da ibtila’i a idanunsa na hagu da hanci a wata arangama da dan wasan baya na Chelsea Antonio Rudiger a wasan karshe cikin gasar zakarun turai a ranar Asabar da ta gabata.
A ranar 12 ga watan Yuni ne Belgium za ta kafza da Denmark da kuma 17 sai ta sake kafzawa da Finland duk a cikin gasar Euro 2020.
Mai horas da yan wasan Belgium Roberto Martinez ya ce tiyatar da aka yi wa de Bruyne bai fi minti 20 ba aka kammala don haka ana sa ran zai murmure nan ba da jimawa ba.