Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya ce rashin tsaro ya tabarbare a karkashin jam’iyyar APP mai mulki.
A wata hira da yayi da BBC Hausa, Makarfi ya ce lokacin da jam’iyyar PDP ke mulki, rashin tsaro ya kasance a yankin Arewa maso Gabas ne kawai amma duk da haka kasar ta gudanar da zabe saboda matakan da gwamnatin da ke mulki ta dauka a lokacin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Ya Jajantawa Gwamnatin Kano Kan Rugujewar Ginin Kasuwar Kantin Kwari
Makarfi, wanda ya mulki jihar Kaduna daga shekarar 1999-2007, ya ce da yawa daga cikin ‘yan Najeriya ba za su iya zuwa gonaki, ko kasuwanni, ko ziyartar ‘yan uwansu ba saboda rashin tsaro a yau.
“Ka yi tunanin abin da ke faruwa a Arewa maso Yamma iri daya a Arewa ta Tsakiya da Kudu. A Najeriya noma ya yi matukar wahala, kasuwanci ya yi wahala, ziyarar ta yi wahala kusan komai yana da wahala a yi shi,” inji shi.
A cewarsa, idan ‘yan Najeriya suka sake baiwa PDP dama jam’iyyar za ta samar da kwakkwaran jagoranci da zai tunkari matsalolin da kuma magance matsalolin.
Ya kara da cewa kalubalen tsaro da jam’iyya mai mulki ta gada daga PDP shi ne rikicin Boko Haram.
“Abin da suka gada shi ne rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas duk da cewa PDP ta riga ta shawo kan lamarin kuma shi ya sa aka gudanar da zaben a Arewa maso Gabas. Ba mu ce saboda rashin tsaro ba za mu iya gudanar da zabe ba amma yanzu ko a jihar Kaduna akwai barazanar cewa ba za a yi harkokin siyasa a wasu wuraren ba da za a yi zabe. Wannan bai taba faruwa a baya ba.”
“Idan kun gaji wani abu a Arewa maso Gabas, ku magance shi amma maimakon magance lamarin yanzu ya tabarbare,” in ji shi.
A kan hanyar fita daga halin da ake ciki, Makarfi ya ce shugabanci nagari da kwazo ne kadai zai iya tinkarar lamarin.
A wani labarin kuma, Yanzu-yanzu: Kotu Ta Wanke Tsohon Gwamna Jang Daga Zargin Almundahanar Biliyan 6.3
Wata babbar kotun jihar Filato da ke zamanta a Jos a ranar Juma’a ta sallami tsohon gwamnan jihar, Jonah Jang, tare da wanke shi daga laifukan almundahanar naira biliyan 6.3 da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa take yi masa
Kotun da ke karkashin mai shari’a Christy Dabup ta kuma sallami wani tsohon mai karbar kudi a ofishin sakataren gwamnatin jihar Filato, Yusuf Pam, wanda aka zarge shi tare da tsohon gwamnan.