Ana sa ran sauran ɓurbushin makamin roka da kasar China ta harba ka iya fadowa zuwa duniya, sai dai ba a san wace duniyar zai faɗa ba.
A watan da ya gabata ne dai kasar ta harba makamin mai cin dogon zango, inda take gwaje-gwaje na makaman ta.
Rokar mai nauyin kilogiram dubu goma sha takwas na ita ce ta roka mafi girma da aka taɓa harbawa tsawon gwamman shekaru da za ta fado duniya ba san inda za ta faɗa ba.
A ranar Alhamis ne Kasar Amurka ta ce tana chan tana hangon rokar, to amma ba ta da aniyar kakkabo saboda gudun tsokalo tsuliyar dodo.
“Fatan mu kawai shine idan za ta fada kada ta fada inda za ta cutar da jama’a, muna fatan ta fada a teku ko kuma wani wuri mai kama da haka” inji Sakataren Harkokin tsaron Amurka Lloyd Austin.
Masana sararin samaniya na ci gaba da hasashen cewa rokar ka iya fadawa yau ko gobe, to sai dai babu hanya daya ta kare kai daga balain ta.