Mai shari’a Inyang Ekwo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma’a ya ba da umarni ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da ta kama tare da tsare mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Amarachi Iwuanyawu bisa zargin almundahanar Naira miliyan 785.
An kuma ce mataimakin shugaban majalisar shi ne shugaban wani kamfani mai suna Sun Gold Estate Limited da ke Abuja, kamfanin da ake zargin ya yi amfani da shi wajen damfarar magudan kudaden na Naira miliyan 785m.
KARANTA WANNAN LABARIN:Nasarawa: PDP Ta Sake Sanya Ranar Yakin Neman Zaben Ta Bisa Umarnin ‘Yan Sanda
Alkalin ya bayar da umarnin ne a ranar Juma’a yayin da yake yanke hukunci a kan karar da shugaban EFCC ya shigar gabansa.
Mai shari’a Ekwo ya bayar da umarnin cewa idan aka kama dan majalisar Imo a tsare shi har zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa inda ake sa ran hukumar yaki da cin hanci da rashawa zata gurfanar da shi gaban kotu.
Takardar da Olarewaju Adeola ya bayar a madadin Shugaban Hukumar EFCC, ta nuna cewa, ana zargin Mataimakin Shugaban Majalisar ne, a shekarar 2012, ya kulla yarjejeniya da wani Kamfani na Abuja, Hokiz Investment Limited.
A cikin yarjejeniyar, mataimakin shugaban majalisar ya yi amfani da kamfaninsa na Sun Gold Estate Limited wajen kulla yarjejeniyar gina rukunin gidaje 14 na benaye guda hudu da kuma katanga daya na gidaje shida a filin Hokiz Investment Limited da ke Mabushi a Abuja.
EFCC ta yi ikirarin cewa bangarorin biyu sun amince cewa kashi 40 na gine-ginen za a bar su ne ga Hokiz Investment Limited kasancewar mai filin yayin da Sun Gold Estate, a matsayin mai ginawa, kuma mallakin Mataimakin Shugaban Majalisar zai rike kashi 60 cikin 100.
Sai dai bayan kammala aikin, an ce Kamfanin Sun Gold Estate Limited ya sayar da dukkan gine-ginen ba tare da sanin mai fili ba.
Kaso 40 na gine-ginen da aka sanya a kasuwa kan Naira miliyan 785, an ce shugaban masu gina gidaje wanda shi ne kakakin majalisar dokokin jihar Imo a yanzu ya yi watsi da su.
Hukumar EFCC ta sanar da kotun cewa ana binciken karar da aka shigar kan mataimakin shugaban majalisar mai dauke da sa hannun Abdullahi Malik (SAN), a madadin wadanda suka yi korafin.
Sai dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta koka da cewa duk kokarin da Amarachi Iwuanyawu ya yi na ganin ya mutunta gayyatar da aka yi masa dangane da zargin ya ci tura, don haka ne aka nemi kotu ta kama shi.
Hukumar EFCC ta yi ikirarin cewa bayanan da ta ke da su sun nuna cewa wanda ake zargin ya tsere zuwa kasar Amurka.
Mai shari’a Ekwo bayan ya binciki abubuwan baje kolin da aka gabatar a gaban kotu tare da gamsassun hujjoji na lauyan EFCC, Olanrewaju Adeola ya bayar da umarnin cewa hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta bi mataimakin shugaban majalissar, ta kama shi a ko ina yake a duniya, ta tsare shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu a ranar 23 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa.
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Dalibai Mata Guda Biyu Bisa Laifin Cin Zarafin Wata Malama
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wasu dalibai mata biyu na makarantar sakandaren Adesuwa da ke Benin bisa zargin cin zarafin wata malamar su.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a garin Benin.
Nwabuzor ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa daliban su ne kan gaba a cikin wadanda ake zargi da tashe tashen hankula da wasu dalibai suka yi a makarantar ‘yan mata a ranar Alhamis.