Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wasu dalibai mata biyu na makarantar sakandaren Adesuwa da ke Benin bisa zargin cin zarafin wata malamar su.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a garin Benin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nasarawa: PDP Ta Sake Sanya Ranar Yakin Neman Zaben Ta Bisa Bin Umarnin ‘Yan Sanda
Nwabuzor ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa daliban su ne kan gaba a cikin wadanda ake zargi da tashe tashen hankula da wasu dalibai suka yi a makarantar ‘yan mata a ranar Alhamis.
“Daliban sun nuna rashin gamsuwa da matakin ladabtarwa da wata malamar makarantar ta dauka a kan wasu dalibai a lokacin da ake karatun harshen Ingilishi,” in ji shi.
Nwabuzor ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo, Mista Mohammed Dankwara, ya tabbatar wa jama’a musamman iyaye da masu kula da daliban makarantar cewa babu wani abin damuwa saboda an dawo da zaman lafiya a makarantar.
Nwabuzor ya kara da cewa “Ya shawarci iyaye da masu kula da wadancan daliban da su mika ‘ya’yansu da unguwannin da ke da hannu wajen tayar da zaune tsayen.”
Kakakin ‘yan sandan ya kuma ce CP din ya umurci jami’in ‘yan sanda reshen Aduwawa da ya mika takardar karar zuwa sashin binciken manyan laifuffuka na jihar Benin a kan kammala binciken farko don ci gaba da bincike.
A wani labarin kuma, Kotu Ta Kori Dan Takarar Gwamnan ADC Da Na Majalisar Dokokin Jihar Ogun
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abeokuta, jihar Ogun ta kori dan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a zaben 2023, Biyi Otegbeye, da kuma ‘yan takarar majalisar dokokin jam’iyyar a jihar.
An dai kori ’yan takarar ne bayan da bangaren jam’iyyar Labour reshen jihar Ogun suka tunkari kotu inda suka bukaci ta tilasta wa hukumar zabe ta kasa INEC kar ta amince da dan takarar gwamna da sauran su.
Mai shari’a Akintayo Aluko wanda ya jagoranci shari’ar, ya tabbatar da cewa zaben fidda gwanin da ya samar da Otegbeye da sauran ‘yan takarar ba a bi dokar zabe ba wajen gudanar dashi.Daga nan ya soke zaben.