Wata babbar kotun tarayya dake zama a birnin tarayya Abuja ta yi barazanar bada umarnin cafke Tsohuwar Ministar sufurin jiragen saman Najeriya Stella Oduah.
Kazalika kotun ba ita kaɗai za a cafke ba har da karin wasu mutane takwas da ake zarginsu da aikata laifuka daban-daban muddin ba su gurfana a gabanta ba a wa’adin da aka diba musu.
Alkalin kotun Mai Shari’a Inyang Ekwo ita ta yi wannan gargadi a ranar Litinin yayin da Misis Oduah da sauran mutane takwas din suka gaza bayyana a zamanta da ta gudanar, ba kuma tare da karin haske kan hakan ba.
Ana tuhumar mutanen tara ne da zargin badakala daban-daban har 25 ta hanyar wadaka da kudi har kimanin naira biliyan goma.