Wani fasto na kasar Kenya kuma wanda ya kafa Cibiyar Neno Evangelism ya shawarci matan da ke zaune a cocinsa suna sauraron wa’azi inda ya ba su mafita kan ‘yan matan mazajensu, LIB ta ruwaito.
A wani wa’azi da ya yi, faston ya ce kada su dinga yi musu fatan mutuwa, su dinga yi musu fatan Ubangiji ya basu nasu mazajen.
KU KARANTA: Amarya ta yanke jiki ta faɗi bayan ango ya yi fatali da soyayyarsu ranar aurensu
A cewarsa:
“Na ji yanzu kun koma yi wa ‘yan matan mazajenku fatan mutuwa. Mata dayawa suna son hakan.
“Maimakon yi musu wannan addu’ar, ku yi musu fatan Ubangiji ya basu nasu mazajen.”
Ng’ang ta kara cewa mata ba su da laifi tunda maza ne dakansu suke fara zuwa su same su. Ya cigaba da cewa:
“Mijinki ne ya dace ya rike miki amana, saboda shi ne mai laifi. Maimakon yi wa ‘yan matansu munanan addu’o’i, me zai hana ki fara halaka mijinki?
“In har dagaske kin tuba ga Ubangiji ya kamata ki san cewa laifuka biyu ba sa taruwa su koma daidai. Ba a hori kiristoci su dinga kisa ba.”
Ku dinga amsa saƙonnin mazan nan, akwai masu shirin aure, Cewar Amaka bayan ta cafko miji a Facebook
Wata Amaka ciki da farinciki ta bayyana wasu kyawawan hotunan shagalin aurenta kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
A cewar Amaka, ‘yan matan da suka san ba su da samari su dinga kula sakonnin mazan da ke turo musu, inda tace akwai mazajen aure da dama a Facebook.