Wani bidiyo da yake karade yanar gizo ya nuna wani fasto yana caccakar mambobin cocin sa bisa bayar da naira ɗari (N100) a matsayin sadaka.
Faston wanda ya caccaki mabiyan nasa yayi magana ne cikin harsuna biyu, turanci da Igbo a yayin da yake faɗan nasa. Jaridar Legit.ng ta rahoto
KU KARANTA KUMA: An yi martani mai zafi kan mutumin da ana huɗuba yana kallon ƙwallo
Faston ya koka da cewa cocin na siyo man fetur domin sanyawa a janareto, inda ya haƙiƙaance kan cewa ko kaɗan bai kamata ace suna bayar da waɗannan ƴan ƙalilan kuɗaɗen ba.
A yayin mayar da martani, ƴan Najeriya d dama sun caccaki faston kan wannan furucin da yayi, inda da yawa daga ciki suke cewa wasu fastocin fa ba mutanen da suke neman yarda wajen ubangiji bane.
Ga kaɗan daga cikin martanin da mutane suka yi waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
Odukale Nifemi Kabirat ta rubuta:
“Maganar gaskiya, waɗanda suka bayar da naira ɗari (N100) sun yi ƙoƙari, duba da yadda abubuwa suke a ƙasar mu yanzu kashe kobo ma wahala yake yi. Na yi tsammanin wannan mai kiran kan shi da faston yayi addu’ar Allah ya ƙara musu yawan lalitar su ta yadda za su bayar da abinda yafi haka nan gaba.”
Eric Mudima Gowal ya rubuta:
“To idan kuma mutum naira ɗarin da take raga masa kawai ya bayar fa? Shin yayi tunanin hakan kuwa?”
Adesegun Ogundeji ya rubuta:
“Ba laifin sa bane. Laifin waɗanda suke ciyar da shi ne. Yaje yayi aiki kawai ya daina yiwa mutane ƙwace.”
Wani Magidanci Ya Siyar Da Kamfaninsa Ya Ginawa Ɗiyarsa Katafaren Wajen Wasa
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci yayi abun ban mamaki ya siyar da kamfanin sa domin farantawa yarinyar sa.
Samun cikakken so da kulawa daga wajen mahaifiya abu ne wanda aka saba da shi amma ya kan fi armashi idan aka ce hakan ya samu ne daga wajen mahaifi.
Hakan shine abinda ya faru da wata yarinya mai ɗauke da wata lallura ta nakasa wacce mahaifinta ya siyar da kamfanin sa kawai saboda jindaɗin ta.