William Henry Gates II, mahaifin hamshaƙin attajirin nan da ya ƙirƙiri kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya rasu a ranar Litinin yana da shekaru 94 a duniya.
Iyalan Henry sun shaidawa jaridar York Times cewa cutar Alzheimer ce ta yi sanadiyar mutuwarsa.
Marigayi William tsohon soja ne kuma yana daga cikin manyan lauyoyin da suka ƙirƙiri wani kamfani da ake kira Seattle law firm.
“Za mu yi kewarsa fiye da yadda ake tsammani. Muna cikin matuƙar baƙin ciki da godiya ga Ubangiji” cewar Bill Gates mai shekara 64 a yayin da ya ke bayyana mutuwarsa a kafar sadarwarsa a ranar Talata.
“Hikimarsa da karamcinsa da fahimtar mutane da kuma rashin girman kai ya taimakawa mutane a duniya baki ɗaya.”
Bill Gates ya bayyana alhininsa musamman ta yadda mahaifinsa ya taimakawa rayuwarsa da ta ƙanwarsa inda ya ce sun yi ‘matuƙar sa’a’ da Ubangiji ya basu iyaye da ke basu ƙwarin gwiwa tare da haƙuri da su.
Ya kuma ce mahaifin nasa shi ne jigon fara Gidauniyar tallafawa al’umma ta Bill & Melinda Gates Foundation da suka ƙirƙira tare da matarsa, Melinda.
“Ba don mahaifina ba, da Gidauniyar Bill & Melinda Gates ba ta kai inda take a yau ba,” inji Bill Gates.
Mahaifinsa shi ya riƙa shugabantar Gidauniyar tallafin tun da aka ƙirƙire ta cikin shekara ta 2000.
Gidauniyar ita ce abin da hamshaƙin attajirin a yanzu ya mayar da hankali a kai bayan ya yi murabus daga shugabancin kamfaninsa na Microsoft.