Kocin Ƙungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist dake birnin Bauchin Yakubu Usman Abdallah Shariff ya ajiye aikinsa a yau Talata.
Da sanyin safiyar yau ne aka wayi gari da wannan sabon labari cikin wata sanarwa da ya fitar kana aka baza wa manema labarai.
Abdallah Shariff ya kuma yaba wa yan wasa da kafatanin hukumar gudanarwar kungiyar bisa zaman amana da suka yi.
Ko da yake har yanzu bai bayyana dalilin ajiye aikin nasa ba, amma wata kila hakan ba zai rasa nasaba da halin Mashashshara da kungiyar ta Wikki Tourist ke ciki ba.
Da ma dai ko da Abdallah bai ajiye aikin nasa ba, akwai gargadi da aka baiwa yan wasan Ƙungiyar cewa muddin ba su lashe wasansu da Plateau United a ranar Lahadi ba, to lashakka za a zabtare albashin su.