Yayin da Manchester City ta kara matsa lamba kan dan wasan Tottenham Harry Kane, a ranar Litinin dan wasan ya gaza bin tawagar kungiyar zuwa filin atisaye.
Da ma an shirya za a yi gwajin korona ma dan wasan a ranar Litinin kafin daga bisan ranar Talata ya yi saɓi zarce zuwa filin atisaye, to amma fa ya ki amincewa da wannan gwaji.
Harry ya share makonni uku yana hutu bayan taimakawa kasarsa ta Ingila zuwa wasan ƙarshe a gasar Euro 2020 da ya gudana a kasar Ingila.
Har kawo yanzu dai ƙungiyar Tottenham ba ta fitar da wata sanarwa kan dalilin da ya sa Kane din ya ƙi fita stisayen ba.
Tun farko da ma dai Kane ya bayyana cewa akwai yarjejeniya tsakaninsa da Shugaban Tottenham Daniel Levy kan cewa zai iya barin kungiyar a kakar nan.
Baya ga Kane dai City ta kwallafa ranta kan Jack Greelish inda baje lalitarta ta ware kuɗi har pam miliyan 100 don dauko shi.