Gwamnatin tarayya ta sanar da karɓar tallafin allurar rigafin korona kimanin miliyan huɗu samfurin Moderna daga kasar Amurka.
Wakilin hukumar kula da asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da kuma Hukumar bada tallafi ta kasar Amurka USAID ne ya mila rigafin wa gwamnatin tarayya a birnin tarayya Abuja ranar Litinin.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa tun ranar Lahadi ne allurar rigafin ta korona ta iso Nigeria.
Idan za a iya tunawa Nigeria ta kaddamar da fara gudanar da allurar koronar ce tun a watan Afirelu, bayan samun kimanin miliyan huɗu samfurin AstraZeneca wanda ke samun tallafin COVAX.
Da ma dai COVAX din na tallafawa kasashe matalauta ne don rage raɗaɗin rayuwa wa kasashen, inda tuni ta tallafa wa kasashe 129 da allurar kimanin miliyan tamanin.
Yanzu haka dai ana ganin allurar ta Moderna da Nigeria ta samu wanda ta samu sahalewa daga hukumar NAFDAC, zai iya taimakawa wajen fadada rigafin da Nigeria izuwa lungu da sakon kasar.
Yanzu haka a Nigeria mutane akalla 2,149 ne suka kwanta dama yayin da 174, 000 suka harbu da cutar ta korona, sai dai ana ganin adadin ka iya zarta haka lura da yadda ake samun karancin gwaje gwaje.