Tsohon mataimakin gwamnan babban Bankin Najeriya (CBN) Obadiah Mailafiya ya ajiye muƙaminsa, saboda kashe-kashen da ake yi a kudancin jihar Kaduna, wanda ya ce yana addbar jama’arsa.
Mailafiya ya sanar da murabus ɗinsa a matsayin Darakta a Cibiyar Horas da Dabarun Mulki (NIPPS) da ke Kuru, Jihar Filato a ranar Litinin.
“Na yanke shawarar ba zan ci gaba da aiki cikin nutsuwa ba alhali ana ci gaba da yi wa mutane kisan ƙare dangi.
“Dalilina na ajiye aiki ke nan kuma kwamitin gudanarwar ya amshi buƙatata; na ba su sanarwar wata ɗaya daga 18 ga Agusta zuwa 19 ga Satumba. Matakin da na ɗauka shi ne mafi a’ala ga kowa”, kamar yadda ya shaidaw manema labarai.
Ya bayyana masa haka ne bayan wakilinmu ya nemi jin ko binciken da hukumar tsaro ta DSS ta yi masa a kwanakin baya na da alaƙa da ajiye aikin da ya yi.
“Na ajiye aiki a NIPPS. Babu wanda ya sa ni ko ya tursasa min. Na yanke shawarar ba zan ci gaba da aiki cikin nutsuwa ba alhali ana ta yi wa mutanena kisan ƙare dangi.
Wani rahoto na cewa Mailfiya ya yi watsi da Hedikwatar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi masa, wanda lauyansa Yakubu Bawa ya ce an mika musu ta Ofishin Mataimakin Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya a ɓangaren binciken manyan laifuka.
Barista Yakubu Bawa ya ce salon gayyatar ya saɓa tsarin da aka saba gani, yana mai zargin alakar gayyatar da tambayoyin da hukumar tsaro ta DSS ta yi wa Mailafiya a kwanakin baya.
A kwanakin baya DSS ta yi wa Mailafiya tambayoyi bayan wata hira da aka yi da shi a gidan radiyo ‘Nigeria Info’ inda ya yi zargin cewa wani gwamna mai ci a Arewacin Najeriya ne shugaban ƙungiyar Boko Haram.
Sauran zarin da ya yi a hirar kan yanayin tsaro a Arewacin Najeriya sun haɗa da cewa bakin ‘yan bindiga da Boko Haram ɗaya kuma jiragensu na ta jigilar makamai da kuɗaɗen a lokacin dokar kulle tamkar babu dokar.
Ya yi iƙirarin cewa yana daga cikin waɗanda suka gana da tubabbaun kwamandojin mayaƙan Boko Haram waɗanda suka shaida masa haka, har ya ce ‘yan bindigar da suka bazu a ko’ina a Najeriya na shirin fara kai hari a cikin birane suna kashe manyan mutane, kuma za su fara yaƙin basasa a 2022.
Kalaman nasa dai sun haifar da muhawara da kiraye-kirayen a yi bincike domin gano gaskiyar zarge-zargen tsohon Mataimakin Gwamnan na CBN.
Bayan fitowarsa daga ofishin DSS ya ce yana kan maganganun nasa da ko kafin nan sun sa an ci tarar gidan Nigeria Info tara.
Daga baya ya fito yana bayar da haƙuri cewa ya ji abubuwan da ya faɗa din ne a bakin wasu mutane da ya haɗu da su a kasuwar ƙauye.