Kwamitin majalisar Dattijan Najeriya kan nazarin kundin tsarin mulkin kasa ya amince da kudirin da aka shigar gabansa na cewa tilas ne Shugaban Kasa ya naɗa ministoci da sauran mukarabbansa cikin wata guda bayan rantsuwar kama aiki.
Kazalika su ma Gwamnoni wannan doka ta wajaba a kansu da su naɗa Kwamishinoni da sauran mukarabbansu ko kuma doka ta yi aiki a kansu.
Wadannan duk na daga cikin kudurori da mambobin kwamitin suka rattaba wa hannu a zamansu na ranar Lahadi.
Yanzu haka kwamitin na jiran rattaba hannun uwar majalisar ce don dokar ta fara aiki.