Kimanin Mako guda kenan bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da Shugaban hukumar jin koken jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, majalisar dokokin jihar ta gayyace shi da ya gurfana a gabanta.
Majalisar ta ce zai gurfana gaban ta ne ranar Laraba don amsa wasu tambayoyi da aka shigar gaban kwamitin binciken wucin gadi na majalisar.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne majalisar ta dakatar da Muhyi Magaji-Rimingado biyo bayan wani korafi da ta samu daga akanta Janar na Jihar.
A ranar Talata ce dai majalisar ta aike masa da takardar sammaci mai dauke da sanya hannun Shugaban Kwamitin harkokin ayyuka na jihar Abdullahi A. Bature Dal.
“An umarce ni da na rubuto maka wannan takarda kan cewa ka zo ka gurfana gaban wannan kwamiti dake bincike kan korafi da aka shigar a kanka, a matsayin na Shugaban Hukumar karbar koken jama’a da yaki da cin hanci da rashawa” cewar sanarwar.
“Kuma ana so ne ka gurfana gaban majalisar a ranar Laraba 14 ga watan Yuli da misalin karfe 12 na rana a harabar majalisar dokokin jihar Kano”
“To sai dai duk da yake an rubuta wannan takarda, amm ba lallai bane a ce Muhyi Magaji-Rimingado ya bayyana gaban majalisar bisa ikirarin rashin mallakar kwafin takardar da ake zarginsa da shi, kamar yadda wata majiya ta shaida.
Comments 2