Malami: Karya ne, Banyi rubutu don aibata kabilar Ibo ba
Shugaban Alkalan Alkalai, Kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya karyata zance da akeyi kan ya wallafa rubutu yana cin mutuncin kabilar Ibo. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta.
Wannan ya fito ne daga bakin mataimakin sa a kafan sada zumunta Umar Gwandu, yace baiyi makamanci zancennan ba.
KARANTA:-Sojoji sun rabama Mutane sama da dubu biyu Magunguna kyauta
Yace shugaban Alkalan Alkalai Kuma Ministan Shari’a bai taba koda da dai ba, da nufin yin rubutu don aibata wata kabila ko wata al’ada ba a wannan kasar.
Yace “Malami an sanshi Mutum ne dan Kasa mai bin doka da oda, mai ganin mutuncin kowa, baya nuna fifiko akan wani ko daga wani kabila ko yanki ya fito, zai mu’amalanceshi da tausayawa da sanin ya kamata.”
Kamar yadda Gwandu yace “Rashin fahimtar turanci da rashin tunani da kuma rashin sanin darajar mutane ne yasa ake dangata Malami da wannan zancen”
Ofishin Ministan Shari’a dai yayi kira ga Jama’a da su jefar da wannan zancen ba gaskiya bane.
Yace an kirkiri wannan zancen ne don cin mutuncin da aibata Ministan Shari’a Abubakar Malami.
Ya kara da cewa kafafen watsa labarai sunyi binciken gaskiya don tabbatar da Malami baida alaka da wannan rubutu, kawai tatsuniya ce, shaci fadi ne.
Comments 1