Majalisar Masarautar Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya ta yanke hukuncin cewa babu maganar hawan Sallah a bana sakamakon barazanar matsalar tsaro da Jihar ke fuskanta.
To sai dai Masarautar ta ce kamar yadda aka saba, hakimai da dagatai da kowace shekara ke hallarowa don hawan daushen za su iya shigowa su gudanar da Sallah amma ba tare da dawakai ba.
Cikin wata sanarwa da Sakataren Masarautar Nasir Musa Maidala ya fitar, ta ce masarautar ta dauki wannan mataki ne a wani taron gaggawa da ta gudanar a yau Lahadi dangane da bukukuwan Sallar dake tafe.
Har ila yau sanarwar ta kara fa cewa gaishe-gaishe da masu rawani suka saba yi musamman izuwa gidan Gwamnati don mika mubaya’a wa Gwamnan Jiha bisa al’ada, tana nan daram, to sai dai wannan karon babu maganar hawa dawaki don mika gaisuwar.