A wani abu da ya kasance tamkar ruwan dare, Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona amma ta mata dake ƙasar Spaniya, ta lashe gasar Laliga ta bana da ake kira da Primera Division.
Wannan shine karo na shida da kungiyar ke lashe wannan, abinda ya sa kungiyar ta fi ko wace kungiya lashe gasar kenan tun bayan kirkiro ta a shekarar 1988.
Sauran Ƙungiyoyin da suka lashe gasar sun hada da Atletico Madrid da ta lashe sau biyar, yayin da Atletico Bilbao ta lashe sau daya.
Kungiya daya da ake ganin za ta iya bajinta ita ce real Madrid to amma ta zama kurar baya, domin ko sau daya ba ta taɓa lashe gasar ba.
A wannan kaka dai ta bana an karkare ne Barcelona da ta zama zakara tana da maki 78, sai mai take mata baya Levante mai maki 62, yayin da Real Madrid ke mataki na uku da maki 61.