Shahararriya jarumar finafinan masana’antar Nollywood, Mercy Aigbe, ta musulunta.
Jarumar tana auren wani babban mai shirya finafinai a masana’antar finafinan ta Nollywood, Kazeem Adeoti.
Mercy Aigbe ta bayyana sabon sunan ta na musulunci a yayin wata lakca da addu’o’i na musamman da ita da mijinta, Kazeem Adeoti, suka shirya. Rahoton jaridar Tribune
KU KARANTA KUMA: Bidiyon wani shirgegen maciji yana shiga cikin tukunyar bahaya ya sanya tsoro a zukatan mutane
Jarumar ta bayyana komawar ta addinin musulunci ne a cikin wani bidiyo inda aka tattauna da ita wanda tuni ya karaɗe shafukan sada zumunta.
Jarumar a cikin tattaunawar ta bayyana sabon sunan ta na addinin musulunci.
“Sabon sunana shine Hajia Meenah Mercy Adeoti. Meenah mai ɗauke da harafin H,” Inji jarumar
Tattaunawar da akayi da ita wacce ta yaɗu sosai a wajen lakcar Ramadan, wacce ta samu halartar manyan jarumai, ta sanya mutane da dama sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi.
Mutane da dama sun yi mata murnar shigowar ta cikin addinin musulunci inda suka yi ta ƙwaroro mata addu’o’i.
Tsohon Dan wasan AC Milan Clarence Seedorf ya Musulunta
A wani labarin da muka taɓa kawo muku, kun ji cewa tsohon ɗan wasan AC Milan, Clarence Seadorf, ya musulunta.
Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Real Madrid, Ajax, Sampdoria da Inter Milan Clarence Seedorf ya karbi kalmar shahada ajiya Alhamis.
Tsohon dan wasan na kasar Netherlands wanda a baya cikakken sunan sa shine, Clarence Cycle Seedorf, Amma bayan ya koma addinin musulunci ajiya ya mayar da sunan sa ya koma Younis.