Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mai kula da gonaki a gonar tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Adebayo Alao-Akala.
Alao-Akala, wanda dan asalin Ogbomoso ne, ya mulki jihar a matsayin gwamna tsakanin shekarun 2007 zuwa 2011.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/majalisar-dattijai-ta-dakatar-da-zamanta-biyo-bayan-mutuwar-dan-majalisa-daga-jihar-edo/
Ma’aikacin gonar wanda dan asalin Gbongan ne a karamar hukumar Ayedaade a jihar Osun, an yi garkuwa da shi ne a gonar mai suna TDB da ke Jabata a karamar hukumar Surulere a jihar Oyo.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro a ranar Talata cewa ma’aikacin, Christopher Bakare. Wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sun yi garkuwa da shi da misalin karfe 7 na yammacin ranar Asabar.
Masu garkuwa da mutanen suna kuma neman abiya zunzurutun kudi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar sa.
Wata majiya ta kusa da dangin Alao-Akala kuma dan asalin Ogbomoso, ta tabbatar wa da Jiridar DAILY POST sacen mutumin a ranar Talata.
Ya ce an kai rahoton lamarin zuwa ga ‘yan sanda.
“Mun yi ta kokarin tattaunawa da su duk da cewa an sanar da ‘yan sanda”.
Wata majiyar ta kara da cewa, an sanar da rundunar ‘yan sandan yankin Ogbomoso game da lamarin.
Sai dai duk kokarin da DAILY POST ta yi don jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso ya ci tura domin kiran da aka yi ta wayar salula bai dauka ba, yayin da sakon SMS da aka aika masa shima bai amsa ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.