Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya koka kan yadda wasu masu satar bayanai daga kasashen waje ke kai hari kan rumbun adana bayanai na hukumar, LIB ta rawaito.
Yakubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi a ranar Alhamis, 26 ga watan Janairu, a wajen taron kungiyar ‘yan jarida ta kasa NAJUC a Abuja mai taken, ‘Zaben 2023; Shari’a da Dorewar Dimokuradiyyar Najeriya.”
KARANTA WANNAN LABARIN: A Cikin Iyalina, Kowa Yana Son Kiɗa – Mr Sab
A cewar shugaban hukumar ta INEC wanda ya samu wakilcin mataimakin daraktan hukumar ta ICT, Dr Lawrence Bayode, ya ce hare-haren sun fito ne daga sassa daban-daban na duniya ba Najeriya kadai ba.
Yace;
“Muna duba tsarin a jiya kuma muna ganin cewa mutane na kokarin shigowa cikin tsarin daga kasar Faransa amma kuma muna sanya wasu abubuwa.
“Ba za ku iya gina gida ba kuma ba za ku sanya kofa, taga ko ɓarna ba; mun yi iya bakin kokarinmu don ganin cewa tsarinmu ya kare.”
Jami’in na INEC ya kuma bayyana cewa, Sakamakon IReV da na baya suna da cikakken tsaro don hana kai hari.
A karshe ya bayyana cewa ba za a yi zabe ba tare da katin zabe na dindindin (PVC) da kuma tantancewa kamar yadda sashe na 47(1) na dokar zabe ta 2022 ya tanada.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Dan Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Rasu
Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya yi rashin dansa na farko.
Hassan Sule, mai shekaru 36, ya rasu ne a yammacin ranar Alhamis.