Matasa sun kama wani mataimakin shugaban makarantar sakandare dumu-dumu yana lalata da dalibarsa, LIB ta ruwaito.
Mutumin wanda shi ne na biyu a matsayi a makarantar sakandare nan Kgagatlou da ke Polokwane, Limpopo ya ci na jaki bayan an kama shi yana lalata da dalibarsa yayin da wasu daliban ke karatu a azuzuwansu.
KU KARANTA: Ɗanjaridar BBC ya ci na-jaki yayin da ya je ɗaukar rahoto ana zanga-zanga
A wani bidiyo da ya dinga yawo a Twitter, sai da suka daure shi jikin ice sannan suka dinga dukansa kamar Allah ya aikesu.
An samu rahotanni kan cewa ba wannan bane karon farko da aka ritsa shi yana lalata kananun yara ba a makaranta.
An raba shi da wata makaranta ne inda aka komai da shi a matsayin mataimakin shugaban makarantar sakandare Kgagatlou.
Mai goge-goge ya ci na jaki a hannun matashin da ya ritsa da yana lalata da budurwa a bayin da zai wanke
Wani mutum ya kai wa mai goge-goge farmaki yayin da ya kama shi yana lalata da wata mace a bayi, LIB ta ruwaito.
Mutumin mai suna Billy Dean Fallon, mai shekaru 28 yana tsaka da lalata da wata mata sai mai goge-goge ya fara kwankwasa kofar bayin, nan da nan ya fito ya fara dukan mai goge-gogen.
Yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotu, a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, ya amsa laifinsa. Hakan yasa aka umarce shi da biyan mai goge-gogen $1,500.