Wani matashi ɗan Najeriya mai suna Austino Ihezue, ya bayyanawa labarin soyayyar sa ga masu amfani da yanar gizo a TikTok.
Austino ya bayyana yadda talauci yayi masa katutu wanda har ya kai shi ga shan kwaki da gishiri a maimakon sukari, sannan ya riƙa tunanin ya kashe kan sa kawai ya huta. Rahoton jaridar Legit.ng
KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga ta ɓarke kan kin amsar tsofaffin kuɗi a wata jiha a Kudancin Najeriya
Sai dai ya samu sauyin rayuwa lokacin da ya haɗu da masoyiyar sa, wata baturiya, wanda har soyayyar su ta kai ga aure.
A kalamansa:
“Rayuwata ta sauya lokacin da na haɗu dake, da ace na kashe kai nayi asarar ɗumbin albarkar da ubangiji ya tanadar min yanzu ba. Kada ku yarda da batun kisan kai sannan ku cigaba da aiki tuƙuru.”
“Nan bada daɗewa ba rayuwar ku zata sauya. Akwai lokacin da talauci yayi min katutu sai da na koma shan kwaki da gishiri shine babban abinci a wajena.”
Mutane da dama sun kaɗu matuƙa da jin labarin wannan matashin, inda suka yi ta masa fatan alheri.
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
n0lst ya rubuta:
“Kai shan kwaki da gishiri akwai wuya
Naji daɗi da Allah ya taimaki rayuwar ka.”
@samuelemmanuel62 ya rubuta:
“Eh dukkan godiya ta tabbata ga Allah, domin indai da rai da rabo. Yanzu ka samu sauyi, godiya ta tabbata ga Allah.”
big_pion33 ya rubuta:
“Lallai naga mutane da yawa nata mamaki a wajen sharhi game da kwaki da gishiri!!! Abinda nima ya riga ya zame min jiki! Allah ka taimake ni.”
Bayan Gama Ɗawainiya Da Ita Na Shekara Huɗu, Budurwata Ta Gujeni -Matashi Ya Koka
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya koka bayan da budurwar da ya kwashe shekaru yana yiwa wahala ta rabu da shi.
Wani matashi ɗan Najeriya ya bayyana yadda budurwar da ya gama ɗawainiya da ita na tsawon shekara huɗu ta rabu da shi.
Ɗan Najeriyan ya bayyana hakan ne a wani rubutu da wani mai amfani da sunan @Sealveeyah2 Twitter, ya wallafa.