Abdulrasheed Bello wanda akafi sani da JJC Skillz, ya dawo addinin musulunci bayan auren sa da jarumar finafinan Kudancin Ƙasar nan (Nollywood) kuma ƴar siyasa, Funke Akindele, ya mutu.
Tun da farko dai an haifi JJC Skillz cikin addinin musulunci amma daga baya ya rikiɗe ya koma addinin da mahaifiyar sa take yi. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Bayan yayi mata fitsarin kwance, wata budurwa ta ɗauki mummunan mataki akan saurayinta.
A wani rubutu da yayi a shafin sa na Instagram, Abdulrasheed ya bayyana cewa a da ya ɓata amma yanzu ya dawo kan turbar gaskiya.
A kalamansa:
“A da na ɓace amma yanzu na dawo kan turba. Ya Allah, ina roƙonka yafiya da lafiya a wannan duniyar da lahira. Ya Allah ina roƙonka yafiya da lafiya a cikin lamarin addini na da na duniya, da iyalai na da dukiya ta. Ya Allah ka lulluɓe kasawata sannan ka sauƙaƙa min daga aukawa cikin masifa. Ya Allah ka kare ni daga baya da gaba, daga hagu da dama, sannan daga sama, a wajen ka nake nema Ya Allah, kada ka bari duniyar nan ta ruɗeni.”
Bayan yayi wannan rubutun nasa, mawaƙin yayi ƙarin haske yayin tattaunawa da majiyar mu inda yake cewa:
An haife ni cikin musulunci. Sunana Abdulrasheed, mahaifina musulmi ne amma mahaifiyata Kirista ce. A baya da ina zuwa Islamiyyah amma abinda naƙe iya tunawa kawai shine yawan shan dukan da nake yi. Suna tsoratar da mu da wutar Jahannama. Sai na ƙi yin addinin.”
“Tsarin Allah ne cewa zan dawo musulunci. Nagode wa Allah da ya bani aron rayuwa. Nayi matuƙar farin ciki na sake samun musulunci saboda ya bani salama. Ya sanya na san inda na sa gaba a rayuwa. A da na ɓace amma yanzu na dawo kan turba.”
Banjin Daɗin Aure Matata Ta Hana Muyi Kwanciyar Aure -Magidanci Ya Koka
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya koka bayan matarsa ta hana shi jindadin rayuwar aure.
Wani magidanci ɗan ƙasar Kenya mai suna James Jkorir ya koka kan yadda matar sa take hanawa suyi kwanciyar aure.
Magidancin ya bayyana cewa yayi nadamar auren matar sa saboda duk lokacin da ya nemi da suyi kwanciyar aure ta fake da cewa bata da lafiya.
Magidancin ya nuna ɓacin ran sa ne dai a wani rubutu da yayi a wani dandali na mabiya addinin Kirista, a ranar Laraba 18 ga watan Janairun 2023.