Hafsan Sojin Najeriya Manjo Janar Farouq Yahaya ya bayyana cewa jami’an rundunar sun gama shan ɗamara na ganin sun kawo karshen matslaar tsaro dake addabar shiyar arewa maso gabas.
Hafsan Sojin yana wannan batu ne yayin wani rangadi ga jami’an rundunar yaki na Operation Hadin Kai a birnin Damaturu na Jihar Yobe.
Ya ce muddin aka kawo karshen Matsalar ta’addancin, to babu wani abu da ya yi saura wa rundunar kuma sai a kama wani batu daban.
Matsalar ta’addancin dai a shiyar alta arewa maso gabas ta daɗe tana ci wa al’umma tuwo a kwarya kimanin Shekara goma kenan ana abu guda, lamarin da kuma ya ɗaiɗaita shiyar.
Farouk Yahaya kara da cewa makasudin rangadin shine son ganewa idanunsa irin ta’adi da Wannan matsala ta yi tare da nemo bakin zarenta.
Da ma dai tun a ranar asabar ne Hafsan Sojin ya ziyarci Sgehun Borno a fadarsa don neman tubarraki da kuma shawarwari irin na iyayen kasa.