Akalla mutane biyu ne suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a wani wurin da tsaffin mayakan Boko Haram ke zaune a Maiduguri na jihar Borno Kamar yadda Daily Trust Ta Ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babu Abunda APC Ta Haifarwa Najeriya Banda Yunwa Da Talauci – Okowa
An bayyama hakan ne ta bakin Zuwaira Gambo kwamishiniyar harkokin mata da cigaban al’umma ta jihar.
Gambo ta ce ma’aikatan lafiya sun tabbatar da asarar rayuka biyu sakamakon cutar.
Da take musanta rahotannin mutuwar da dama da aka yi, ta nace cewa “mutane biyu ne kawai suka mutu”, ta kara da cewa alkaluman da aka ambata kan lamarin ba su da tushe.
Ta ce, “Ban san daga ina wannan adadi ya fito ba, amma ina tabbatar muku cewa abin da muke da shi mutuwa biyu ce kawai.”
A cewarta, jami’an ma’aikatar lafiya ta jihar sun koma cibiyar domin kwashe wasu da suka kamu da cutar kwalara domin keɓe su.
Kwalara cuta ce mai saurin kamuwa da gudawa ta hanyar kamuwa da kwayar cutar Vibrio cholerae daga hanji.
Mutane na iya yin rashin lafiya lokacin da suka haɗiye abinci ko ruwan da suka gurbace da kwayoyin cutar kwalara.
A WANI LABARIN KUMA: Na Gama Nasara a Zaben 2023 Lokacin Rantsuwa Nake Jira – Dan Takarar Shugaban Kasar PRP
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PRP, Kola Abiola, ya bayyana cewa zai lashe zaben shekara mai zuwa ta hanyar maimaita irin rawar da mahaifinsa, Marigayi MKO Abiola ya yi a zaben 12 ga watan Yuni, 1993.
Kola ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a Abeokuta, ranar Asabar a wajen bikin jana’izar marigayi dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Ogun, Farfesa David Bamgbose.