Kamfanin dake kula da man fetur na Kasa NNPC ya ce kimanin matasa dubu uku ne za su samu aiki a yayin gyaran matatar man fetur na Fatakwal.
Wata sanarwar daga shugaban kamfanin kuma na shiya, Dakta Kennie Obateru ya ce a yanzu haka an kammala duk shirye-shirye da suka kamata na ganin an cimma nasarar wannan aiki ba tare da tsaiko ba.
Da yake tsokaci yayin taron kaddamar da fara aikin, Jami’i Mai kula da matatar man, Injiniya Yakubu Mustapha ya ce a yanzu babu abinda ya rage a kasa da ba a yi ba, wanda da zarar an fara aikin to lallai ba zai tsaya har sai an ci galaban shi na kusan kashi 90 kana ya fara aiki.
“Za mu tabbatar sa cewa babu algus a cikin wannan aiki, shi ya sa ma muke janyo mazauna wannan yanki a jika don su amfana, duk hankulan Yan Najeriya ya karkata a kan mu, don haka ta ya kuke ganin za mu watsa wa mutane kasa a idanu” Cewar shi.
Da yake jawabi ta bakin jami’in harkokin kudi Mista Umar Ajiy, Shugaban Kamfanin NNPC Mallam Mele Kyari ya ce yan Najeriya su kwantar da hankalin su domin aikin zai kammala kana a fara tace mai gabannin ko kuma daga ranar 5 ga watan Afirelun 2023.