Bisa kokari da ake ci gaba da yi na shawo kan bazuwar annobar korona a duniya, an bada zabin cewa ba kuma za sake yiwa baligai da ba daranma shekara 40 allurar rigafin Korona ta AstraZeneca ba.
Hukumar Kula da Ingancin Magunguna ta Kasar Birtaniya ta ce a yan baya bayan nan an samu rahoton daskarewar Jini daga mutane 242 cikin mutane miliyan 28.8 da aka yi musu rigafin, kuma ta ce hakan ya fi illa ne kan masu ƙarancin shekaru.
Kazalika yanayin raguwar karin mutane da suka kamu da cutar na daga cikin Musababbin da ya sa aka dauki matakin dakater da rigafin wa matasa.
Rigafin Kamfanin AstraZenecan ya gamu da cikasa na daskarewar Jini ga duk wanda aka mishi, duk da cewa bai taka kara ya karye ba.
Ko wane mutum guda cikin dubu dari da aka yi wa rigafin na fuskantar fama da daskarewar Jini cikin kankanin lokaci bayan an yi mishi ko da yake daga bisani ya koma cikin mutane dubu sittin