Mutane 5 ne suka mutu tare da lalata gidaje 3,813 sakamakon ruwan sama da aka yi a wasu kauyuka a kananan hukumomi 13 na jihar Katsina.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ce ta bayyana hakan a ranar Litinin din na.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na SEMA, Malam Umar Muhammad, ya ce mutane uku sun rasu a karamar hukumar Kankara da kuma wasu mutane biyu a karamar hukumar Mai’adua.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kakakin hukumar ta SEMA ya bayyana cewa gwamnatin jihar na yin iya kokarinta wajen ganin an dakile afkuwar ambaliya a jihar, inda ya kara da cewa, an kafa wani kwamiti kan bada agajin gaggawa domin dakile bullar cutar kwalara a sakamakon ambaliyar.
Karanta kuma: Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar yaran Mai Unguwa 4 a jihar Katsina
Ya ce, “A karamar hukumar Kankara, gidaje 176 ne abin ya shafa, a Danja, gidaje 125, sai Kankia gidaje 86, da Katsina gidaje 620, da kuma Musawa gidaje 482, da Batagarawa 361, yayin da Kusada gadaje 311sai Sabuwa gidaje 111.
“A karamar hukumar Zango, an lalata gidaje 105, a Batsari kuma gidaje 443, da Funtua gidaje 258, sai Safana gidaje 581 da karamar hukumar Ingawa kimanin gidaje 154 biya lalace.
“Hakazalika, gidaje 176 sun lalace sannan mutane uku sun rasa rayukansu a bala’in da ya faru a Kankara yayin da gidaje 154 suka lalace a Ingawa.”
Gidan talabijin na Channels ya rawaito, Muhammad ya kuma lissafa karin kananan hukumomi guda biyar wadanda suka hada da; Mashi, Mani, Mai’adua, Dandume da Matazu wadanda bala’in ya rutsa da su, inda hukumar SEMA ta kasa tantance yawan barnar da aka yi.
A wani labarin kuma: Sojoji Na Gudanar Da Bincike, Haɓakawa Don Magance Kalubalen Tsaro A Kasa
Rundunar Sojin Najeriya ta jaddada kudirinta na gudanar da bincike da ci gaba don magance kalubalen tsaro da ke addabar al’ummar kasar yadda ya kamata.
Mejo janaral Abdulsalam Ibrahim, Shugaban Horaswa (Sojoji) ya sake nanata hakan a wajen bude taron bincike da ci gaba na shekarar 2022 da daidaita tsarin karatu ga Makarantun Sojojin Najeriya a ranar Litinin din nan a Abuja.