By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutum daya a garin Igbaye dake karamar hukumar Odo-Otin a jihar Osun bayan wani bikin shakatawa da aka gudanar wanda ake zargin ya rikide zuwa zubar da jini.
An tattaro cewa wasu matasa ne suke gudanar da bukukuwan murna a garin a ranar Litinin da yamma lokacin da rashin fahimtar juna ya barke tsakanin wasu kungiyoyi biyu a cikin al’umma.
Yayin da wata majiya ta bayyana cewa rikicin na da nasaba da rikicin masarautar al’umma yankin, inda wani mazaunin garin ya ce bikin ne kawai yasa dangan takar tayi tsami tsakanin matasan garin.
Wani shaidan gani da ido, Rasheed Damola ya ce rikicin ya fara ne a filin wasan shakatawa bayan gardama ta barke tsakanin wasu kungiyoyi biyu a wurin taron kuma lamarin ya rikide zuwa na ‘yanci.
“Wasu mutane dake wurin sun fara jifa da kwalabe, kulake da duwatsu kamar wadanda suka halarci taron sun yi kaca-kaca da su domin tsira da rayukansu. Kwatsam sai ga wasu mutane suka fara harbe-harbe inda aka samu mutum guda a cikin lamarin. Wanda yasa tuni aka garzaya da shi wani asibiti a Okuku kuma ya mutu kafin a kai ga zuwa asibitin” in ji shi.
Sai dai wata majiya mai suna Atanda Adeola ta bayyana cewa, abin da ya jawo rikicin shi ne batun masarautar al’ummar yankin, inda ya kara da cewa bikin wani uzuri ne kawai na sake farfado da rarrabuwar kawuna a kan kujerar sarautar garin.
“An samu rikici kan kujerar al’umma wanda jam’iyyu basu manta da su ba tsawon shekaru, don haka, lokacin da ‘yar ta kaddamar rashin fahimtar juna ta kaure tsakanin wasu kungiyoyi game da sarautar sun dauki rikicin suka fara harbin juna. Inda ta kai ga kashe daya daga cikinsu,” in ji shi.
Sai dai kuma yunkurin kiran basaraken na garin ya ci tura domin an ce lambar wayarsa akashe take.
A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola da yake tabbatar da faruwar lamarin, yace an tura ‘yan sanda domin dawo da zaman lafiya a cikin al’ummar da ke fama da rikici.
Sai dai yace ba’a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba amma ya bayyana cewa ‘yan sanda sun maido da doka da oda a garin kuma suna ci gaba da sa ido kan al’umma.
“Tun daga lokacin kwamishinan ‘yan sanda, Mista Olawale Olokode ya ba da umarnin tura jami’ai zuwa garin kuma an dawo da zaman lafiya,” in ji shi.