Wata budurwa mai karancin shekaru ta bayyana yadda ta lale kudadenta ta biya sadakinta kamar yadda ta bayyana yadda lamarin ya auku, Legit.ng ta ruwaito.
Budurwar mai shekaru 34 mai suna Zuku ta kammala makaranta da satifiket uku inda iyayenta suka lashi takobin amsar dukiya mai yawa daga duk matashin da yazo aurenta.
KU KARANTA: Duk wata sai saurayina ya bani sama da N11m don in gyara kaina, Budurwa
Yayin bayyana wa News24, Zuku ta cewa ita da kanta ta yanke shawarar biyan sadakinta.
A cewarta:
“Idan wani ya sanar da ni cewa a shekaru 34 ni zan biya sadakina zan yi dariya ne kawai. Amma kawai sai ga shi, ni da kaina na biya. Ba zan yi karya ba. Na ji kunya.”
A al’adar Afirka, aikin miji ne samar da sadakin auren budurwar da yake so. Amma a wannan karon an samu sauyin yanayi.
Zuku ta ce ta fi saurayin da za ta aura kudi wanda hakan ya sanya ta yanke shawarar taimaka masa wurin biyan kudin sadakin aurenta.
Budurwa ta tashi saurayi a Twitter bayan ya ce ya shirya aure amma babu matar aure
Wata mata a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba ta tashi wani matashi a Twitter yayin da ya bayyana cewa yana da zone amma bai samu budurwar da zai nemi aurenta ba, LIB ta ruwaito.
Abin ya fara ne bayan wani kwararre a harkar soyayya ya bukaci wadanda su ka yi aure da su gabatar da hotunan aurensu.
Sai dai matashin ya wallafa hoton zobe a hannunsa inda yace na aure ne amma har yanzu be samu matar da zai aura ba.